in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya tana tsara matakan sake dawo da motocin Hyundai
2019-01-25 09:19:16 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, mahukuntan kasar sun tanadi wani tsari ta yanar gizo don hanzarta dawo da motocin kamfanin Hyundai da za a sake musu injuna, inda za a ake saran dawo da motocin ta hanyoyi biyu da aka tanada a baya.

Babban darektan hukumar kare 'yancin masu sayayya a Najeriya (CPC) Babatunde Irukera ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, motocin da ake shirin dawo da su, sun hada da Hyundai Sonata kirar 2011-2014 da Hyundai Sonata Fe Sport kirar 2013-2014.

Iruke ya kara da cewa, kamfanin Hyundai dake kasar Amurka ya sanar a ranar Laraba cewa, za a kara dawo da motocin kamfanin don a kara duba yadda aka makala bututun man motocin da aka ambata a baya, wadanda a baya aka dawo da su don magance matsalar da ka iya haddasa rashin aikin injinunan motocin.

Ya ce, za a duba motoci na baya-bayan da ake shirin dawo da su ne, a kuma tabbatar da cewa, an sake sanya babban bututun da zai iya zuko mai yadda ya kamata.

Shugaban hukumar ta CPC ya kara da cewa, kamfanin yana son ya inganta fasahar kula da injunan motocinsa da sabuwar nau'ra da ke iya sansano duk wata matsala.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China