in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin-gwiwar Sin da Najeriya ta fannin tattalin arziki da kasuwanci na bunkasuwa yadda ya kamata
2019-01-30 15:50:47 cri
A wajen taron shekara-shekara na kamfanonin kasar Sin dake Najeriya wanda aka yi a jiya Talata a Abuja, an bayyana cewa, a shekarar da ta gabata, hadin-gwiwar Sin da Najeriya ta fannin tattalin arziki da kasuwanci ta samu bunkasuwa cikin sauri kuma yadda ya kamata, haka kuma jimillar kudin cinikayyar kasashen biyu ta kai dala biliyan 15.3, wanda ya karu da kashi 10.8 bisa dari idan aka kwatanta da na shekara ta 2017. Najeriya ta ci gaba da zama babbar kasa ta farko a nahiyar Afirka, inda ake samun kamfanonin kasar Sin dake zuba jari a kasar, kana, ta zama babbar kasa ta biyu a Afirka wadda kasar Sin take fitar da kayayyakinta. Bugu da kari, Najeriya ta zama babbar aminiyar kasuwanci ta uku ta kasar Sin a nahiyar ta Afirka.

Taron kamfanonin kasar Sin dake Najeriya na shekara ta 2018, wanda sashin kula da harkokin tattalin arziki da kasuwanci na ofishin jakadancin Sin dake Najeriyar ya dauki nauyin shiryawa, ya samu halartar jakadan Sin dake Najeriya, Zhou Pingjian, da babban jami'in kula da harkokin tattalin arziki da kasuwanci na kasar Sin Zhao Linxiang, gami da wakilai daga kamfanonin kasar Sin daban-daban a Najeriyar, ciki har da kamfanin CCECC, da CGC da Huawei da sauransu.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China