A wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu a jiya Laraba, kakakin rundunar wanzar da tsaro ta musamman ta Operation Sharan Daji, Clement Abiade, ya ce dakarun sun yi arba da babbar tawagar mayakan 'yan bindigar dake dauke manyan makamai na zamani a dazukan Dumburum da Gando ranar Lahadi.
A 'yan shekarun baya bayan nan jahar Zamfara, tana fuskantar kalubalolin tsaro musamman a yankunan karkarar jahar, wanda a baya ake samun kwanciyar hankali amma a yanzu ake fuskantar rikici tsakanin makiyaya da manoma.
Hare haren da 'yan bindigar suka kaddamar a jahar Zamfara ya yi sanadiyyar hallaka rayukan gomman mutane kana wasu dubbai suka tsere daga gidajensu tun a watan Disambar shekarar 2018.
A watan Disambar gwamnatin Najeriya ta tura karin jami'an tsaro, da jirgin saman yaki na sojoji zuwa jahar ta Zamfara da jahar Sokoto mai makwabtaka domin fatattakan mayakan masu dauke da makamai. (Ahmad Fagam)