in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
INEC ta lashi takwabin magance yin magudi a zabukan kasar dake tafe
2019-01-23 09:46:08 cri
Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya (INEC) ta sanar da cewa, tana kokarin tabbatar da cewa, ba a aikata magudi ba yayin manyan zabukan kasar dake tafe.

Da yake karin haske cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai a Abuja, fadar mulkin kasar, mai magana da yawun hukumar Rotimi Oyekanmi ya bayyana cewa, hukumar za ta tabbatar da cewa, an gudanar da zabe cikin adalci da kowa zai lamunta da shi.

Ya ce, a bisa tsarin hukumar ta INEC, wajibi ne duk wanda ya cancanci kada kuri'a ya gabatar da katinsa na kada kuri'a na din-din-din (PVC) a tantance shi, sannan na'ura ta tabbatar da cewa katinsa ne kafin ya kai ga kada kuri'arsa.

A cewar hukumar, ta bullo da matakan tantance mai kada kuri'a da ma yin zabe a lokaci guda ne, saboda masu sa-ido na cikin gida da kasashen duniya da suka kalli yadda manyan zabukan kasar na shekarar 2015 sun ba da shawarar yin amfani da shi.

Bayanan hukumar dai na zuwa ne, bayan da aka tabbatar da cewa, sama da masu kada kuri'a miliyan biyu ne ba su dawo sun kada kuri'unsu ba, bayan da aka tantance su, saboda wasu dalilai. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China