in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Najeriya tana zargin babbar jam'iyyar adawar kasar kan dakatar da yakin zabenta
2019-01-27 16:57:04 cri
A jiya Asabar gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa matakin da babbar jam'iyyyar adawar kasar ta dauka na dakatar da yakin neman zabenta ta yi hakan ne domin yunkurin kare kanta, saboda dama dai yakin neman zaben nata ya riga ya mutu tun tsawon lokaci da ya wuce.

Jam'iyyar adawa ta PDP ta sanar a ranar Asabar cewa, ta jingine yakin neman zabenta na tsawon kwanaki uku, domin nuna adawa da dakatarwar da gwamnatin kasar ta yiwa babban mai shari'a na kasar Chief Justice Walter Onnoghen, bisa zarginsa da aikata laifin take doka na kin bayyana kaddarorinsa.

Minsitan yada labarai da raya al'adu na kasar Lai Mohammed, ya mayar da martani kan matakin da jam'iyyar adawar ta dauka, yana mai cewa, jam'iyyar PDPn tana rusa kuka ne fiye da matar da ta rasa mijinta.

"Ni ban gane ba, me zai sa su ba mu hutu," Mohammed ya fadawa 'yan jaridu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da dakatar da Justice Onnoghen ne, har zuwa lokacin da za'a kammala shari'ar da ake masa a kotun da'ar ma'aikata.

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa Uche Secondus, ya ce sun dakatar da yakin neman zaben ne domin nuna adawarsu tare da sauran 'yan Najeriya bisa abin da ya kira cin zarafi ga tsarin demokaradiyya.

To sai dai kuma, ministan yada labaran ya ce, matakin da PDPn ta dauka abin zargi ne. "Suna yin wani abu tamkar dama akwai wani boyayyen al'amari tsakanin jam'iyyar da korarrar babban alkalin, idan ba haka ba, mene ne zai sa su dakatar yakin neman zaben wanda dama tun tuni ya jima da mutuwa," in ji Lai. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China