Mataimakin kakakin babban sakataren MDD Farhan Haq ne ya bayyana hakan yayin taron majalisar da aka saba gudanarwa, yana mai cewa wannan adadi ya hada da mutane miliyan 1.8 da tuni suka gujewa matsugunan nasu a yankin arewa maso gabashin kasar.
Jami'in ya ce, su ma kungiyoyin kasa da kasa da hukumomin bayar da agaji sun nuna damuwarsu game da illar da karuwar tashin hankali da matsalar tsaro ka iya haifarwa, a daidai gabar da ake shirin gudanar da zaben shugabancin kasar a ranar 16 ga watan Fabrairun dake tafe, ciki har da karuwar zirga-zirgar jama'a da karancin ayyukan jin kai a wasu yankunan.
A don haka MDD ke kira ga dukkan bangarorin da rikicin ya shafa, da su kare fararen hula da dukiyoyinsu kana su mutunta dokokin kasa da kasa. (Ibrahim)