Jami'in watsa labaru a fadar firaministan kasar Birtaniya Rob Macpherson ya bayyanawa 'yan jarida cewa, Birtaniya da kungiyar EU sun cimma daidaito a karshe, amma ba a bayyana abubuwan dake cikin yarjejeniyar ba.
Jami'in ya bayyana cewa, firaministar kasar Birtaniya Theresa May za ta shugabanci taron majalisar ministocin kasar a yammacin yau, don yi musu bayani game da abubuwan dake kunshe cikin yarjejeniyar da ma shirye-shiryen da za a aiwatar a nan gaba.
A halin yanzu, kafofin watsa labaru na kasar Birtaniya sun maida hankali sosai ga batun iyakar kasar da Ireland a cikin yarjejeniyar ficewar Birtaniya daga kungiyar EU. Firaministar kasar Birtaniya ta taba bayyanawa a watan da ta gabata cewa, an kammala kashi 95 cikin dari na shawarwarin ficewar Birtaniya daga EU, batun iyakar kasar da Ireland shi ne kawai ba a cimma daidaito a kai ba. (Zainab)