in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sudan ya yi gargadi game da duk wani yunkurin da zai tada hankali a kasar
2019-01-28 10:53:52 cri
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir dake ziyara a kasar Masar, ya ce akwai wasu masu mummunar manufa dake yunkurin yi wa zaman lafiya da tsaro a kasarsa tarnaki.

Omar al-Bashir ya bayyana haka ne jiya a birnin Cairo, yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na Masar Abdel Fattah al-Sisi.

Jawabin na shugaba al-Bashir na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsaka da zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar, wanda aka fara tun tsakiyar watan Disamban bara. A cewar kwamitin kasar da aka dorawa nauyin gudanar da bincike kan zanga-zangar, al'amarin ya yi sanadin mutuwar mutane 29.

Cairo shi ne wuri na biyu da shugaban na Sudan ya ziyarta bayan ziyarar da ya kai birnin Doha a baya-baya nan, tun bayan da zanga-zangar ta barke a wurare daban daban na kasar, ciki har da babban birninta wato Khartoum, sanadiyyar tabarbarewar yanayin tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyakin bukata.

A nasa bangaren, shugaba Sisi ya ce tattaunawarsa da shugaba Bashir ya mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi dangantakar kasashen biyu da dangantakar tattalin arziki da kuma wasu batutuwan da suka shafe su. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China