in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan zai kai ziyara Qatar duk da zanga zangar da kasarsa ke fuskanta
2019-01-22 10:39:00 cri
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir zai isa birnin Doha a yau Talata, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Qatar (QNA) ya sanar a jiya Litinin.

Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, yana sa ran zai gana da al-Bashir a fadarsa a gobe Laraba domin tattaunawa da shi game da kyautata alakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma wasu batutuwa da suka shafi bangarorin biyu, in ji kamfanin dillancin labaran na QNA.

Ziyarar ta al-Bashir zuwa Doha ita ce ta farko tun bayan da zanga zanga ta kaure a kasar Sudan a ranar 19 ga watan Disambar 2018, inda jama'ar kasar ke bore don nuna bacin ransu kan tabarbarewar tattalin arziki da tsadar kayayyaki a kasar.

Da yake jawabi a ranar Lahadi ga dandazon magoya bayansa a jihar White Nile, mai tazarar kilomita 392 a kudu maso yammacin babban birnin kasar Khartoum, shugaban ya fada cewa, al'ummar Sudan su ne ke da ikon yanke shawara kan wanda zai shugabance su ta hanyar kuri'a. Kuma shekarar 2020 ba wani lokaci ne mai nisa ba, in ji shi. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China