in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ya ce masu hura wutar zanga zanga su ne suke hallaka masu zanga zangar
2019-01-21 10:48:08 cri
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya bayyana a jiya Lahadi cewa, wadanda ke daukar nauyin shirya zanga-zanga a kasar su ne suke kashe masu zanga zangar da nufin ruruta wutar rikici a kasar.

"Daga cikin masu zanga zangar, akwai wadanda ke hallaka masu zanga zangar," al-Bashir ya furta hakan ne a lokacin da yake jawabi ga taron gangamin jama'a a ranar Lahadi a Al-Kireida yankin dake bangaren jihar White Nile ta kasar Sudan, mai tazarar kilomita 392 a kudu maso yammacin Khartoum, babban birnin kasar.

"Wani likita dake Buri mai makwabtaka da jihar, an hallaka shi da makami wanda ba irin wanda jami'an tsaron kasar ke amfani da shi ba ne, kuma babu irin makamin a fadin kasar Sudan," in ji al-Bashir.

Ya ce "akwai mabiya Abdul-Wahid Mohamed Nur (shugaban 'yan tawayen 'yantar da al'ummar Sudan a Darfur) wanda aka kama shi, kuma ya fada da bakinsa cewa aikinsu shi ne kashe masu zanga-zanga domin kara ruruta wutar rikicin."

A ranar 19 ga watan Disamba, wasu yankuna da dama a Sudan, ciki har da Khartoum, suka fara fuskantar zazzafar zanga-zanga domin nuna bacin ransu game da matsalolin tabarbarewar tattalin arziki da tashin farashin kayayyakin masarufi a fadin kasar.

A bisa ga alkaluman da gwamnatin kasar ta fitar, a kalla mutane 26 ne aka kashe a lokacin zanga zangar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China