Rahoton ya ce, majalisar dokokin kasar ta amince da tsawaita dokar tabaci ne a jihohin kasar biyu zuwa ranar 20 ga watan Yunin shekarar 2019.
Majalisar ta bada hujjar tsawaita wa'adin dokar tabacin ne sakamakon yadda ake samun yawaitar safarar mutane, makamai, da fataucin miyagun kwayoyi da kuma yadda ake kara samun yawaitar makamai a jihar Kassala.
A ranar 30 ga watan Disambar shekarar 2017, shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya ayyana dokar tabaci a jihohin North Kordofan da Kassala. (Ahmad Fagam)