Gwamnatin ta ce, ta samu wasu sahihan bayanai dake tabbatar da cewa wasu daga cikin 'yan adawar siyasa suna ta yunkurin haddasa tashe-tashen hankula a duk fadin kasar domin kawo cikas ga zaben kasar wanda za'a fara a watan gobe.
Da yake jawabi ga 'yan jaridu, ministan yada labaran Najeriyar Lai Mohammed ya ce, gwamnati ta samu wasu sahihan bayanai dake cewa mayakan 'yan tada kayar baya da na Boko Haram suna shirye-shiryen kaddamar da munanan hare-hare da ta da hargitsi a wasu jahohin kasar.
Kakakin gwamnatin Najeriyar ya ce, akwai wasu jahohin arewaci da tsakiyar Najeriyar da ake son kaddamar da hare-haren
Babbar jam'iyyar adawar kasar (PDP), tun a ranar Lahadin da ta gabata ta yi gargadi cewa akwai tashe-tashen hankula a wasu daga cikin jihohin Najeriyar, gabanin gudanar da zabukan kasar. (Ahmad Fagam)