in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kenya: Ba a jingina tashar jiragen ruwa ta Mombasa don biyan bashi daga wajen kasar Sin ba
2018-12-29 17:06:46 cri
A kwanan baya, an yi ta yada jita-jita game da yadda kasar Kenya ta jingina mallakar tashar jiragen ruwa ta Mombasa ga kasar Sin a matsayin biyan bashi. Game da haka, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya ce, wannan magana ce marar tushe.

Uhuru Kenyatta ya bayyana haka ne a yayin da yake amsa tambayoyin manema labaru a birnin Mombasa na kasar, inda ya ce, layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi hanyar layin dogo ce da ba mu taba samu ba a tarihi. Muna amfani da bashin dake kanmu don raya manyan kayayyakin more rayuwa, wannan ba kawai zai samar da alfanu ga jama'ar kasar na yanzu bane, har ma zai kawo tasiri mai kyau ga jama'ar kasar masu zuwa a nan gaba.

Ban da wannan kuma, Uhuru Kenyatta ya bayyana cewa, ko da yake bangarori daban daban sun yi zargin cewa, bashin da kasar Kenya take ci ba zai dore ba, amma kasar zata ci gaba da neman rancen kudi daga sauran kasashe, ciki har da kasar Sin. Saboda akwai wajibci na neman rancen kudi don biyan bukatun duk kasashen dake fatan kyautatta manyan ayyukan samar muhimman kayayyakin more rayuwa.

A cewar Uhuru Kenyatta, "cin bashi ba matsala ba ce, abu mai muhimmanci shi ne, yaya za a yi amfani da bashin. Ko a yi amfani da bashin don neman ci gaba, ko a yi amfani da bashin don inganta GDP, ko kuma a yi amfani da bashin don bude kofa. Kashi 60 bisa dari ne kawai na al'ummar kasar Kenya ke iya amfani da wutar lantarki, wannan ne dalilin da ya sa muke nemo rancen kudi, za mu kuma ci gaba da neman rancen kudi."

Game da tambayar ko rancen kudi da kasar Kenya ta samu daga wajen kasar Sin zai kawo illa ga Kenya ko a'a, Uhuru Kenyatta ya ce, kasarsa bata dogaro kan kowace kasa ba. A cewarsa, yanzu Kenya na kokarin hadin kai da abokan huldarta wadanda ke fahimtar bukatunta na neman ci gaba, kasar Sin ma na daya daga cikinsu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China