in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar zaben Najeriya ta shirya caf don gudanar da babban zaben kasar dake tafe
2019-01-18 09:32:05 cri
Hukumar zabe mai zaman kan ta a Najeriya INEC, ta ce ta kammala dukkanin shirye shirye, na gudanar babban zaben kasar dake tafe a watan Fabarairu.

Cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafin ta, INEC ta ce ya zuwa yanzu, tana karasa daukar wasu matakai ne na tabbatar da nasarar gudanar da sahihin zabe, wanda kowa zai amince da shi.

Da yake tabbatar da hakan, shugaban hukumar Mahmood Yakubu, ya ce an tanaji dukkanin kayayyaki masu nauyi da za a bukata yayin zaben, kaza lika an riga an mikawa ofisoshin hukumar na jahohi takardun kada kuri'u, da akwatunan zabe, da rumfunan zaben, da na'urar zabe madadin wadanda suka lalace, da kuma katunan dindindin na masu kada kuri'u domin al'umma su karba.

Bugu da kari, Mahmood Yakubu ya ce hukumar sa ta fitar da tsarin gudanar da zaben ga al'ummar kasar, kana ta tsara kundin horaswa na ma'aikatan da za su jagoranci zaben.

Ya ce zaben zai kasance sahihi, kuma INEC za ta bi diddiginsa, ta tabbatar an bi ka'ida ta yadda dukkanin 'yan kasar za su amince da shi.

Bisa jimilla, 'yan takara 22,643 daga jam'iyyun kasar 91 ne za su fafata a zabukan kujeru 1,504 yayin zaben na wata mai zuwa.

Wannan adadi ya hada da na 'yan takarar shugabancin kasa 73, da na masu neman kujerar gwamna su 1,158, a jihohin kasar 29. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China