Taken shirin "Bunkasa koren yanayi," shirin na bangarori ne masu zaman kansu, inda masu zuba jari na kasashen Najeriyar da Brazil za su hada gwiwa don zuba jari tare da yin aiki tare karkashin shirin, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ne ya fitar da rahoton.
Shirin dai an tsara shi ne ta yadda za'a samar da cibiyoyin da kwararru za su dinga bada horo, wanda ya shafi yadda za'a hada taraktocin noma da sauran injinan aikin noma da cibiyoyin sarrafa kayan amfanin gona inda kuma za'a dinga samar da muhimman kayan aikin gona, inji mataimakin shugaban kasar Najeriya Yemi Osinbajo.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana aikin a matsayin wani muhimmin mataki a kokarin da kasar ke yi na kawo sauye sauye a sha'anin aikin gonan kasar.
A halin yanzu noma shi ne babban abin da Najeriya ta fi mayar da hankalinta a yunkurin da take na fadada hanyoyin bunkasa tattalin arzikin kasar.
Ana saran za'a aiwatar da shirin a dukkan kananan hukumomin Najeriya 774. (Ahmad Fagam)