in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta sha alwashin dakile safarar bil adama
2019-01-22 09:43:51 cri
A jiya Litinin Najeriya ta yi alkawarin fara wani gangamin wayar da kan al'umma a duk fadin kasar domin dakile laifukan safarar bil adama.

Julie Okah-Donli, darakta janar ta hukumar haramta safarar bil adama ta Najeriya, ita ce ta yi wannan alkawari a Abuja, babban birnin kasar.

Okah-Donli ta fadawa manema labarai cewa, Najeriya ta lura da illolin dake tattare da safarar bil adama kuma za ta dauki matakai kan dukkan wadanda ake zargin su na da hannu wajen aikata wadannan laifuka.

A cewar Okah-Donli, hukumar ta ceto mutane 10,000 wadanda suka fada komar masu safarar bil adama kuma ana ci gaba da sauya tunanin wadanda aka ceto din tun bayan kafa hukumar a shekarar 2003. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China