in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masani: Kasar Sin za ta kasance kasa mafi samun kudin shiga nan da shekarar 2025
2019-01-22 14:45:46 cri
Tsohon mataimakin shugaba kana babban masanin tattalin arziki a bankin duniya Justine Yifu Lin ya bayyana cewa, nan da shekarar 2025, kasar Sin za ta kasance mafi samun kudin shiga, kana nan da shekarar 2030 kasar ta Sin za ta kasance kasa mafi bunkasar tattalin arziki a duniya.

Lin ya bayyana hakan ne yayin taron da aka yi taken "Tattalin arzikin kasar Sin a sabon zamani" taron da shirin samar da ci gaban harkokin kudi mai dorewa a Turai ya karbi bakunci.

Jami'in ya danganta hasashensa ne kan alkaluman GDPn kasar a shekarar 2008 daidai da kaso 21 cikin 100 na kasar Amurka a lokacin, adadin da kasar ta Japan ke da shi a shekarar 1951, daidai da na kasar Singapore a shekarar 1977, da na yankin Taiwan na shekarar 1975 da kuma na Koriya ta kudu a shekarar 1977.

Duk wadannan alkaluma tattalin arziki da aka ambata a sama, sun bunkasa ne tsakanin kaso 8 zuwa 9 cikin 100 a kowace shekara har tsawon shekaru 20 masu zuwa. Ya kara da cewa, wasu kalubale kamar ra'ayin ba da kariya ga harkokin cinikayya da yakin ciniki za su iya rage bunkasar tattalin arzikin. Koda yake, a matsayinta na kasa mai karfin tattalin arziki kana kasa mai matsakaicin kudin shiga, yadda kasar Sin take daukar matakan ginawa da inganta muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a, ya share mafa fage na samun masu sha'awar zuba jari a cikin kasar. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China