Da take jawabi a lokacin babban taron tattalin arziki a birnin Berlin, Merkel ta yi alkawarin cewa, gwamnatin Jamus za ta samar da karin kudade ga kamfanonin kasarta a matsayin inshora domin kaucewa barazanar siyasa da haddarorin dake cikin harkokin cinikayya a kokarin kyautata cinikin Jamus a kasashen waje.
A shekarar da ta gabata, Merkel ta kaddamar da wani gagarumin shiri da nufin fadada hanyoyin zuba jarin kasarta a Afrika a matsayin wani bangare na manufofin fadar shugaban kasar Jamus karkashin shiri cinikayya karkashin kungiyar G20. Domin kyautata dangantakar tattalin arziki a tsakaninta da kasashen Afrika a matakin farko, Jamus tana ci gaba da daukar matakai na sassauta kudaden inshora a kanana da matsakaitan masana'antun cikin gida (SMEs), a yayin da take yin mu'amalar ciniki da kasashe da shiyyoyin duniya da suka rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar cinikayyar. (Ahmad Fagam)