Bisa wannan shirin, sakamakon tabarbarewar yanayin tsaro da kasashen biyu ke ciki, sojojin da Jamus za ta aike zuwa Afghanistan za su karu daga 980 zuwa 1300, kana wadanda za su shiga shirin kiyaye zaman lafiya na MDD a Mali su ma za su karu daga 1000 zuwa 1100. Baya ga haka, gwamnatin Jamus, ta tsaida kudurin aika sojoji zuwa Baghdad, babban birnin kasar Iraki. (Bilkisu)