Merkel ta yi hira da 'yan kasar Jamus fiye da 50 game da makomar kasar, inda ta ce ana bukatar kungiyar EU ta raya dangantakar abota tsakaninta da kasashen Afirka don hana bakin hauren kasashen tafiya nahiyar Turai.
Merkel ta bayyana cewa, kasashen Afirka suna iya kwashe bakin hauren da suka shiga nahiyar Turai ba tare da samun izni ba, kana kasashen Turai sun shirya samar da damar karatu da aiki ga 'yan ciranin kasashen Afirka dake son zuwa Turai bisa doka.
Merkel ta kara da cewa, abu ne mai wuya a cimma yarjejeniyar bakin haure da kasashen Afirka, amma Turai tana bukatar irin wannan yarjejeniya. Ta ce ya kamata kasashen Turai su gudanar da wasu ayyuka don sa kaimi ga bunkasa nahiyar yadda ya kamata.
Merkel za ta gana da shugaban kasar Nijer Mahamadou Issoufou a ranar 15 ga wannan wata a kasar Jamus, inda za su tattauna batun bakin haure. (Zainab)