A sakon ta'aziyyar da ya aiki a Abuja, babban birnin Najeriya a ranar Laraba, shugaban Najeriya ya jajantawa gwamnati da al'ummar kasar Kenya, inda ya bayyana harin da cewa mummunan laifi ne, wanda wasu mutane bata gari suka aikata.
Buhari ya bukaci al'ummar kasashen duniya da su tallafawa kasar ta Kenya domin kawo karshen karuwar ayyukan ta'addanci a kasar, a cewar shugaban " duk wani harin ta'addanci da aka kaddamar kan wata kasa guda daya tamkar hari ne kan dukkan kasashen duniya."
Adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar harin ta'addancin da aka kaddamar kan otel da manyan shagunan a Nairobi ranar Talata ya kai mutuna 21, hukumar 'yan sanda kasar ne ta sanar a daren ranar Laraba.
Kungiyar mayakan 'yan ta'adda ta al-Shabab dake da sansaninta a kasar Somalia ta dauki alhakin kai harin. (Ahmad Fagam)