Jami'an hukumar yaki da rashawa na Kamaru (CONAC) da na hukumar yaki da rashawa ta Najeriya (EFCC), sun gana a Yaounde a jiya Laraba domin tsara wasu ka'idojin yin hadin gwiwa tare.
"Mun zo wannan waje ne da nufin samun fahimtar juna game da danganta, da musayar shawarwari a tsakaninmu," Mohammed Abba Umar, daraktan gudanarwar hukumar EFCC, shi ne ya bayyana hakan ga 'yan jaridu.
"Rashawa ba matsala ce ta kasa daya tilo ba, sai dai matsala ce da ta shafi dukkan kasashen Afrika baki daya, kuma mun yaba da irin hadin gwiwa dake tsakanin Kamaru da Najeriya," in ji shugaban hukumar ta CONAC, Dieudonne Massi Gams.
Badakalar kudaden haram tsakanin kan iyakokin Kamaru da Najeriya na ci gaba da karuwa kuma akwai bukatar a gaggauta daukar matakan dakile su tare da cafke wadanda ke da hannu, in ji jami'an. (Ahmad Fagam)