in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin ruwan Libya sun ceto mutane 14 a wani jirgin ruwa a tashar ruwan Tripoli
2019-01-06 15:40:18 cri
Dakarun tsaron tekun Libya sun samu nasarar ceto wasu matukan babban jirgin ruwa su 14 a tashar ruwa ta Tripoli a ranar Larabar da ta gabata bayan da jirgin ruwan ke kokarin kifewa sakamakon matsananciyar kadawar igiyar ruwan teku da kuma rashin kyawun yanayi.

"Jirgin ruwan mai suna Atlantis, yana dauke da tutar kasar Liberia yana tangal-tangal sakamakon matsalar da yake fuskanta a tekun saboda tsananin kadawar igiyar ruwa a lokacin da jirgin ruwan ke kokarin shiga tashar ruwan Tripoli," ofishin tattara bayanai na sojojin ruwan kasar Libyan ne ya sanar da hakan.

Jirgin ruwan ya bugi wani dutse inda ruwa ya taba injinsa, a cewar sanarwar.

Dukkan matuka jirgin su 14 a ceto su, wadanda dukkansu Indiyawa ne. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China