in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Libya ta yi Allah wadai da harin da 'yan adawar Chadi suka kai wa sojojin kasar
2018-12-28 09:51:52 cri
Gwamnatin kasar Libya dake samun goyon bayan MDD, ta yi Allah wadai da harin da 'yan tawayen kasar Chadi suka kaddamar kan wani sansanin soja dake kudancin Libya, inda suka kashe soja guda tare da jikkata wasu sojojin 6, baya wasu da dama da 'yan tawayen suka yi garkuwa da su.

Wata sanarwa da gwamnatin hadakar kasar ta fitar, ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan hari na matsorata da 'yan tawayen suka kaddamar jiya Alhamis a sansanin soja na Traghen dake kudancin kasar ta Libya.

Gwamnati ta ce, an shirya kai harin ne da nufin wargaza zaman lafiya da tsaron kasar, da ma keta huruminta.

Sanarwar ta ce, yankin kudancin kasar zai kasance mafarin matakan da ake dauka na yaki da ta'addanci da masu neman mayar da hannun agogo baya, har sai an ga bayansu.

Jiya da safe ne dai, 'yan tawayen kasar Chadi suka kaddamar da hari kan wani sansanin soja dake kudancin kasar Libya, harin da ya kai ga kisa da ma jikkatar wasu sojoji, kamar yadda jami'in garin Traghen Abdussalam Shangla ya shaidawa wata tashar talabijin a yankin.(Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China