Wata sanarwa da UNSMIL din ta fitar, ta ce hakan wata kakkarfar alama ce da ke nuna cewa, muddin al'ummar Libya suka hada karfi da karfe, suna iya murkushe kungiyar IS, tare da shawo kan tarin kalubale dake addabar kasar.
Kakakin rundunar sojojin kasar mai helkwata a gabashi Ahmad al-Mesmari ya tabbatar da cewa, sojoji sun kaddamar da hare-hare kan mayakan IS dake yankunan kudancin kasar, inda suka kubutar da mutane da dama da kungiyar ke tsare da su.
A watan Nuwambar shekarar da ta shude ne dai dakarun kungiyar IS suka kaddamar da samame a wasu ofisoshin 'yan sanda, da gine-ginen gwamnati dake Tazirbu, inda suka hallaka mutane takwas, suka raunata wasu 15, kana suka yi awon gaba da wasu da dama.
A watan Oktoba kuma mayakan suka farwa garin Fug'ha dake gundumar Jufra, mai nisan kilomita 650 kudu maso gabashin birnin Tripoli, inda suka hallaka mutane biyar, kana suka sace wasu mutanen da dama. (Saminu Hassan)