A cewar wani jami'in hukumar sufuri na yankin Xizang mai cin gashin kansa, kawo shekarar 2020, dukkan garuruwa da suke da yanayin da ake bukata da kashi 80 na kananan hukumomin za su ci gajiyar ayyukan motocin bus.
Jami'in ya kara da cewa, ginin titin zai taimakawa yankin wajen rage talauci da kara kudin shigar manoma da makiyaya.
Bisa yawan jarin da aka zuba a wannan bangaren, a yanzu tsawon titi a yankin Xizang ya kai km 60,421 idan aka kwatanta da km 53,244 da ya kasance a shekarar 2012. (Fa'iza Mustapha)