in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar 'yan sandan Birtaniya ta bayyana hadarin mota a kofar majalisar dokokin kasar a matsayin aikin ta'addanci
2018-08-15 11:02:38 cri

Kafar yada labarai ta kasar Birtaniya ta ruwaito cewa, rundunar 'yan sandan kasar na ganin hadarin motar da aka yi a gaban ginin majalisar dokoki dake birnin London da safiyar jiya, a matsayin aikin ta'addanci.

Hukumar 'yan sandan London ta bayyana cewa, da safiyar jiya Talata da misali karfe 7 da rabi, wata mota mai launin azurfa ta kutsa kai cikin mutane, inda daga bisani ta ci karo da sandar rigakafi dake wajen ginin, lamarin da ya haddasa jikkatar mutane 3, sai dai babu asarar rai.

Hukumar ta ce, matukin matashi ne mai shekaru 20, kuma an tsare shi bisa laifin aiwatar da ta'addanci, inda ta ce babu wani fasinja a motar, haka kuma bindiga a ciki.

Hukumar kula da zirga-zirga ta birnin London ta ce, an riga an rufe tashar jirgin kasa ta karkashin kasa ta Westminster dake kusa da ginin.

Rahotanni na cewa, a ranar 22 ga watan Maris na bara, an taba aikata irin wannan hatsari a wurin, inda wani direban mota ya kutsa kai cikin mutane a gadar Westminster, da ba shi da nisa daga wannan gini, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5, ciki hadda direban, yayin da wasu 40 kuma suka jikkata. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China