in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Libya ya nemi a sassautawa kasarsa takunkumin hana shigo da makamai
2018-12-26 09:27:11 cri
Ministan harkokin wajen kasar Libya Mohamed Sayala, a jiya Talata ya nanata bukatar sassautawa kasar takunkumin kasa da kasa na hana shigar da makamai kasar Libya domin samun nasarar tabbatar da tsaron kasar.

Sayala, ya yi wannan kiran ne a lokacin taron manema labarai na hadin gwiwa tare da ministan harkokin cikin gidan kasar Fathi Bashagha, a Tripoli babban birnin kasar, sa'o'i kadan bayan wani mummunan harin da aka kai a helkwatar ma'aikatar harkokin wajen kasar wanda ya yi sanadiyyar kashe rayuka da jikkata wasu da dama.

"A shirye muke mu ci gaba da fadi tashin neman a sassautawa kasarmu takunkumin hana shigo da makamai cikin kasar. Ba za mu taba iya aiwatar da duk wani shirin wanzar da tsaro ba muddin ba'a dage mana takunkumin hana shigo da makamai kasar ba," in ji ministan. "Dole ne kasashen duniya su sa baki idan har da gaske suke kan batun yaki da ta'addanci."

Sayala, ya bayyana cewa dukkan wasu muhimman takardu da suka shafi ma'aikatar suna nan ba su lalace ba, ya tabbatar da cewa ma'aikatar za ta dawo bakin aikinta a ranar Laraba a helkwatar wucin gadi. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China