in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afrika sun himmatu wajen warware matsalar 'yan gudun hijira
2019-01-17 09:58:59 cri
A karkashin jagorancin kungiyar tarayyar Afrika (AU), kasashen Afrika, sun sha alwashin daukar matakan warware matsalolin rashin tabbas game da batun 'yan gudun hijira da wadanda rikici ya raba su da matsugunansu.

An cimma wannan matsaya ne bayan sanya hannu da mambobin kasashen 55 na AU suka yi a taron da suka gudanar a helkwatar MDDr dake Addis Ababa, na kasar Habasha, a taron wakilan kwamitin dindindin na kungiyar (PRC) karo na 37, a ranakun Talata da Laraba.

Taron na PRC, wanda aka shirya karkashin jadawalin babban taron kungiyar karo na 32 wanda za'a gudanar a ranakun 10-11 ga watan Fabrairu, yayi karin haske game da batun yanayin da ake ciki kan batun 'yan gudun hijirar Afrika da wadanda tashin hankali ya raba da gidajensu, mai taken: "'Yan gudun hijira, Wadanda suka koma gidajensu da mutanen da rikici ya daidaita: Matakan samar da mafita da kaucewa raba mutanen Afrika da muhallansu."

Taron na wuni biyu, an shirya shi ne karkashin ajandar taron kolin AU tare da bayyana muhimman shawarwari wanda shugabannin majalisar zartaswar AU za su gudanar a taron da za su yi tsakanin 7-8 ga watan Fabrairu, wanda zai samu halartar ministocin kasashen wajen mambobin na AU. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China