Jami'in wanda ya bayyana hakan yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce, yayin da kungiyar ta AU take kokarin ganin yarjejeniyar ta tabbata, ana kuma daukar matakan da suka wajaba na ganin an samar da kasuwar bai daya ta nahiyar da za ta kunshi sama da mutane biliyan 1.2.
Jami'in na AU ya bayyana cewa, yanzu haka kasashe 49 mambobin kungiyar sun sanya hannu kan yarjejeniyar ta AFCFTA, kana kasashe 13 sun ma fara aiki da ita, yayin da wasu 12 kuma sun yi nisa wajen samun amincewa fara amfani da yarjejeniyar daga majalisun dokokin kasashensu. (Ibrahim Yaya)