Daratkan samar da kayayyakin more rayuwa da makamashi na AU, Cheikh Bedda, shi ne ya yi wannan kira a ranar Juma'ar da ta gabata, a lokacin kammala taron tattaunawa kan manufofi da yadda za'a aiwatar da shirin na PIDA wanda aka gudanar da taron a helkwatar kungiyar mai mambobi kasashen Afrika 55 a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.
Ya bayyana cewa PIDA wata hanya ce da za ta taimaka wajen bunkasa ci gaban nahiyar, daraktan ya ce, "PIDA ya kasance a matsayin wani muhimmin shiri mafi dacewa wanda zai taimaka wajen bunkasa ci gaban ababen more rayuwa a fadin nahiyar."
Kashi na 2 na shirin PIDA, zai kunshi mata da matasa, kuma zai shigar da al'ummomi mazauna yankunan karkara domin ba su damar su bada tasu gudunmawar wajen bunkasa ci gaba nahiyar, in ji shi.
Daraktan ya ce abokan huldar Afrika sun fara fahimtar cewa nahiyar tana da irin nata salon da kuma abubuwan da ta fi mayar da hankali kansu wadanda dole ne a mutunta su, kasancewar sun yi daidai da manufofin ajandar AU na raya kasashen nahiyar Afrika nan da shekarar 2063. (Ahmad Fagam)