Sanarwar da ofishinsa ya fitar a birnin Nairobi, ta ce Raila Odinga dake zaman babban wakilin AU kan inganta ababen more rayuwa a nahiyar Afrika, zai bude taron kan shirin raya ababen more rayuwa a Afrika PIDA.
Sanarwar ta ce tsohon Firaministan na kasar Kenya, zai bayyana burinsa game da shirye-shiryen ayyuka da lalubo albarkatu da hanyoyin samar da kudi domin raya ababen more rayuwa a Afrika.
Zai kuma bayyana ra'ayinsa game da cimma hade ababen more rayuwa a nahiyar da sauran wasu batutuwa.
Shugaban hukumar AU Moussa Faki Mahmat, ya ce nadin da aka yi wa Raila Odinga, wani bangare ne na yunkurin AU na gaggauta cimma burin dunkulewar nahiyar ta hanyar ababen more rayuwa, domin inganta ci gaban tattalin arziki da samun dauwamammiyar ci gaba.
Ya ce Raila Odinga zai yi aiki wajen taimakawa tare da karfafa kokarin sassan hukumar AU dake da ruwa da tsaki kan batun, da kuma wadanda dake shiryawa da kula da harkokin hukumar kula da kawancen raya kasashen Afrika, karkashin tsare tsare shirin raya ababen more rayuwa a nahiyar. (Fa'iza Mustapha)