Francisco Madeira, wakilin musamman na kungiyar AU a Somalia, ya ce harin wanda mayakan al-Shabab suka kaddamar, wanda bai samu nasarar kaiwa inda suka so ba, hakan alamu ne dake nuna cewa mayakan ba su nuna tausayi ga rayuwar bil adama.
Abubuwan fashewa 7 ne mayakann suka harba sansanin na AMISOM a ranar Talatar, sai dai dukkaninsu ba su yi nasarar kaiwa inda suka so su kai ba.
Wasu ma'aikatan MDD 2 da wani dan kwangila guda sun samu raunuka a lokacin kai harin na sari ka noke a ranar Talata bayan da mayakan suka harba abubuwan fashewar 7 a harabar ginin MDD.
Kungiyar 'yan ta'adda ta al-Shabab sun dauki alhakin kaddamar da harin. (Ahmad Fagam)