Rahotanni na cewa, zaman na 37, na wakilan dindindin na kungiyar AU, ya gudana ne karkashin tsarin ayyukan taron kungiyar AU na 32, wanda zai gudana tsakanin ranekun 10 zuwa 11 ga watan Fabarairu mai zuwa.
Taken taron dai shi ne "'yan gudun hijira, masu dawowa gida, da wandanda ke samun mafaka a yankuna makwafta: Samar da managarcin tsarin warware kalubalen masu gudun hijira na nahiyar Afirka,".
Bayan kammalar taron na yini biyu, ana sa ran amfani da sakamakonsa wajen tsara ajandar taron manyan jami'an kungiyar ta AU da ke tafe, tsakanin ranekun 7 zuwa 8 ga watan Fabarairu mai zuwa.
Da take karin haske game da hakan, mataimakiyar shugaban hukumar zartaswar kungiyar Kwesi Quartey, ta ce ko shakka babu, yawaitar yake-yaken basasa, da sauran rikice-rikice na kabilanci tsakanin al'ummun Afirka da dama, na tilasawa mutane kauracewa muhallansu, yayin da da yawa ke gudun hijira a kasashe makwafta.
Kwesi Quartey, wadda ke wannan tsokaci yayin bude taron, ta ce a bana, kungiyar AU za ta maida hankali ga batutuwan 'yan gudun hijira da suka rasa matsayinsu na kasar haihuwa, da wadanda suka rasa matsuguni. A cewarta mafi yawan kalubalen da ake fuskanta na da nasaba da rashin nagartattun gwamnatoci, da batun 'yancin bil Adama, da kuma kin martaba dimokaradiyya. (Saminu Hassan)