A jiya Talata ne mambobin majalissar sun jefa kuri'un amincewa da sharuddan 202, da kuma na kin amincewa da su 432, bayan kwashe kwanaki biyar ana tafka muhawara. Manazarta dai na cewa wannan ne karon farko da gwamnatin kasar ta fuskanci rashin nasara mafi tsanani tun bayan shekarun 1920.
Firaministar Birtaniya Theresa May na da kwanaki uku, kafin komawa majalissar da wani tsarin na daban, domin neman amincewarsu. Bisa tsarin da ake da shi a kasa, Birtaniya za ta kammala ficewa daga tarayyar Turai ne a ranar 29 ga watan Maris mai zuwa.
Da take tsokaci game da halin da ake ciki, uwargida May, ta ce duk kwanan duniya kasar tana kara shiga rudani, muddin ba a kai ga warware matsalar da ake ciki ba.
Shi kuwa wani masani game da siyasar kasar Dr. Alan Wager, cewa ya yi sakamakon da ya tabbatarwa gwamnatin kasar rashin nasara, ya wuce wanda aka yi tsammani, kana hakan ya jefa kasar cikin wani yanayi na babban rashin tabbas. (Saminu Hassan)