in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministar Burtaniya ta samu nasara a kuri'ar yanke kauna da aka kada da babban rinjaye
2018-12-13 09:56:06 cri
A jiya Laraba ne firaministar Burtaniya Theresa May ta yi nasara a kuri'ar yanke kauna da 'yan jami'arta na Conservative suka kada da babban rinjaye.

Rahotanni na cewa, Madam May ta samu kuri'u 200 cikin 317 da aka kada a asirce, matakin da ya ba ta damar ci gaba da zama shugabar jam'iyyar ta Conservative.

Da yake sanar da sakamakon kuri'ar, Graham Brady ya ce, sakamakon ya nuna cewa, jam'iyyar tana goyon firaministar. Brandy dai shi ne shugaban kwamitin nan na 1922 wanda ya shirya kada kuri'ar, bayan samun kuri'u 48 na 'yan majalisar da ake bukata kafin kada kuri'ar yanke kaunar.

Majalisar dai ta kaure ta Shewa bayan bayyana sakamakon kada kuri'ar da Madam May ta yi nasara da gagarumin rinjaye. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China