in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministar Burtaniya ta tabbatar da dage kada kuri'a game da ficewar kasar daga EU
2018-12-11 09:48:06 cri
A jiya Litinin ne firaministar Burtaniya Theresa May, ta tabbatar da cewa, ta dage wata kuri'a mai muhimmancin da ya kamata majalisar dokokin kasar ta kada game da ficewar kasar daga kungiyar tarayyar Turai (EU).

Sai dai kafin Madam May ta sanar da dage zaman kada kuri'ar, kudin kasar na Fam ya yi faduwar da ba a taba ganin irinsa ba cikin watanni 18.

'Yan sa'ao'i bayan da 'yan majalisar suka tsaya kai da kafa na ganin an ci gaba da shirin kada kuri'ar a daren ranar Talata kamar yadda aka tsara, Uwargida May ta shaidawa 'yan majalisar canjin da aka samu. Ta ce akwai 'yan majalisar dake adawa da batun iyakar Ireland. Idan kuma har aka ci gaba da kada kuri'ar a ranar Talata, za ta fuskanci gagarumin koma baya.

Madam May ta ce, za ta shirya tattaunawar gaggawa da shugabannin EU game da yiyuwar canja wannan tsari. Ta kuma shaidawa 'yan majalisar cewa, za a iya cimma rashin yarjejeniya da Turai ta hanyar cire shadarar nan ta shinge a cikin yarjejeniyar.

Yayin da Burtaniyar ke shirin ficewa daga kungiyar EU a ranar 29 ga watan Maris na shekarar 2019, wajibi ne majalisar dokokin Burtaniyar ta kada kuri'a a ranar 21 ga watan Janairu don martaba wa'adin dokar shirin ficewar kasar daga EU. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China