Muchanga ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yayin bikin kaddamar da makon raya masana'antu na AIW, wanda zai gudana a helkwatar kungiyar ta AU dake birnin Addis Ababan kasar Habasha, da nufin bankado hanyoyin kara bunkasa tattalin arzikin nahiyar Afirka, da gudanar da sauye sauye a tsarin.
Mr. Muchanga ya kara da cewa, daya daga dalilan da suka gurgunta manufar raya masana'antun Afirka, baya na samun 'yancin kan mafi yawan kasashen ta shi ne, yadda aka fi maida hankali ga shigo da hajoji, da musayar su da kayan sarrafawa da nahiyar ke da su, maimakon fitar da kayayyakin da masana'antun nahiyar ke iya samarwa.
To sai dai duk da haka a cewar jami'in, yanzu haka hankulan kasashen nahiyar na karkata ga inganta darajar kayayyaki, da hajojin da nahiyar ke da su, ta yadda za ta zamo babbar kasuwa ta kasa da kasa, karkashin yarjejeniyar AfCFTA, baya ga burin nahiyar na inganta kayayyakin da take samarwa, ta yadda za su yi takara da makamantan su a kasuwannin duniya. (Saminu Alhassan)