in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun haramta hada-hadar itacen girki a shiyyar arewa maso gabashin kasar
2019-01-14 09:56:32 cri
A jiya Lahadi rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da haramta shigo da itacen girki da gawayi zuwa jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Bulama Biu, mai rikon mukamin babban kwamandan runduna ta 7 (GOC) ta sojojin, ya tabbatar da hakan a Maiduguri, babban birnin jihar, ya ce sojojin sun gano wasu kayayyakin aiki na mayakan Boko Haram wadanda ake amfani da masu safarar gawayin don shigar da su jihar ta Borno.

Ya kara da cewa, wasu bayanan sirri sun nuna cewa, wasu daga cikin manyan diloli a Maiduguri suna fakewa da kasuwancin itacen girki inda suke agazawa ayyukan mayakan 'yan ta'addan.

Ya ce wasu daga cikinsu 'yan koron kungiyar Boko Haram ne, ya kara da cewa, suna boye kayan abinci, magunguna, da man fetur da sauran kayayyaki, inda suke boyewa a cikin manyan motocin, da nufin kaiwa ga mayakan 'yan ta'addan.

"Mun gano wasu daga cikinsu suna kasuwanci ne a madadin mayakan Boko Haram," in ji jami'in sojojin, ya kara da cewa, sun yi cikakken bincike a dazuka inda mutanen asali suke wannan sana'ar ta saran itacen girki da neman gawayi, sun tabbatar wasu na hada baki da mayakan na Boko Haram. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China