Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, kakakinta Ibikunle Daramola, ya ce jirgin na aikin taimakawa sojin kasa na bataliya ta 145 dake aikin sintiri a Damasak dake arewacin jihar ta Borno ne lokacin da ya bace. Jami'in rundunar sojojin Najeriya ya ce ana ci gaba da tattara bayanai game da hadarin jirgin na sojoji.
Daramola, ya kara da cewa, bataliyar na aiki ne da ya shafi dakile ayyukan kungiyar Boko Haram, a yankin dake arewa maso gabashin Najeriya, yankin da tun daga shekarar 2009, ke shan fama da tashe tashen hankula masu nasaba da ayyukan kungiyar, wadda ke da'awar fafutukar kafa daular Islama.(Saminu)