Da yake tabbatar da rasuwar sojojin cikin wata sanarwa, kakakin bataliya ta 145 dake garin Damasak na jihar ta Borno Ibikunle Daramola, ya ce "ina matukar alhinin bayyana rasuwar sojojinmu biyar, dake cikin jirgin yaki na sojoji kirar Mi-35M, wanda ya yi hadari a Damasak dake jihar Borno". To sai dai kuma sanarwar ba ta yi wani karin haske game da wannan batu ba.
A wani ci gaban kuma, rundunar sojojin Najeriyar ta yi watsi da wani rahoto dake cewa, mayakan kungiyar ta Boko Haram na amfani da kayan yaki na zamani, wadanda suka fi na sojojin Najeriya inganci. Rundunar ta ce ana yada wannan farfaganda ne domin yakar tunanin mutane, da kuma yunkurin dakushe karsashin sojojin dake yaki da 'yan ta'addan.(Saminu)