in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan Najeriya sun tabbatar da kai hari kan 'yan ta'adda a jihar Zamfara
2018-12-31 15:03:36 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, mayakan saman kasar sun yi nasarar lalata maboyar 'yan ta'adda tare da kashe da dama daga cikinsu a jihar Zamfara dake yankin arewa maso yammacin kasar, biyo bayan hare-hare na baya-bayan nan da 'yan ta'addan ke kaiwa kan fararen hula da ba su san hawa ba lalle sauka

Mai magana da yawun sojojin saman kasar Ibikunle Daramola wanda ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa, ya ce, an kai samamen na ranar Jumma'a da jijjifi ne, sakamakon wasu rahotannin sirri da ke nuna cewa, mayakan na amfani da wuraren wajen kaddamar da hare-hare.

Sanarwar ta kara da cewa, daga bisani sojojin kasa sun mamaye maboyar mayakan inda suka yi nasarar gano Babura da 'yan ta'addan suka bari.

Daruruwan mutane ne dai suka rasa rayukansu a hare-haren dake da nasaba da gungun 'yan ta'addan cikin wannan shekarar kadai a jihar ta Zamfara dake yankin arewa maso yammacin kasar. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China