in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutune 20 sun mutu a Najeriya yayin da wata babbar mota ta fada kan taron jama'a
2019-01-14 09:38:37 cri
A kalla mutane 20 ne aka tabbatar da mutuwarsu bayan da wata babbar mota ta kauce hanya inda ta fada cikin wata kasuwa mai cunkoson jama'a da yammacin ranar Asabar a jihar Ekiti dake kudancin Najeriya, wasu jami'an yankin da shaidun gani da ido ne suka tabbatar da faruwar lamarin a jiya Lahadi.

Direban babbar motar, wanda ya dauko buhunan shinkafa, ya gaza sarrafa motar ne inda kuma motar ta kwace zuwa cikin wata babbar kasuwa ta Iworoko, kamar yadda Caleb Ikechukwu, kakakin hukumar 'yan sandan jihar Ekiti ya tabbatar da hakan.

Shaidun gani da ido sun fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, sun ga gawarwakin mutane a kalla 20 bayan da jami'an aikin ceto suka tattaro su.

Wani da ya ganewa idonsa faruwa lamarin mai suna Bisi Ayedun, ya ce yawancin wadanda hadarin ya rutsa da su 'yan kasuwa ne dake saye da sayarwa a wajen kasuwar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China