in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
EU zata tura tawagar manyan jami'anta don sa ido kan babban zaben da zai gudana a Najeriya
2019-01-13 16:59:38 cri
Kungiyar tarayyar Turai wato EU zata tura wata tawagar manyan jami'anta zuwa tarayyar Najeriya, don sa ido kan babban zaben da zai gudana a wata mai zuwa.

Bisa wata sanarwar da kamfanin dillancin labaran Xinhua ya samu a ranar Asabar, an ce, EU ta na da wata 'yar siyasar kasar Belgium mai suna Maria Arena a matsayin babbar 'yar kallo ta tawagar ma'aikatan EU masu sa ido kan zabukan da zasu gudana a Najeriya a ranar 16 ga watan Fabrairu da ranar 2 ga watan Maris din bana.

EU ta jibge wannan tawaga ne biyo bayan goron gayyatar da hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriyar wato INEC ta ba ta.

Sanarwar EU ta ce, tun a ranar 4 ga watan Janairun bana, wata tawagar dake kunshe da wasu manazarta zabe su 11 na EU ta isa Najeriya, kuma zata ci gaba da aiki a kasar har bayan kammala zaben.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China