Tuni a ranar Asabar, aka bude taron dandalin tattaunawa tsakanin kasashen Afirka na shekara ta 2018 a birnin Sham el-Sheikh dake bakin tekun Bahar Maliya wato Red Sea na Masar, wanda ya samu halartar shugabannin kasashe membobin kungiyar kawancen kasashen gabashi da kudancin Afirka ta samar da yankin ciniki cikin 'yanci ko kuma COMESA a takaice, inda shugaba Sisi ya ce kasashen duniya na ganin Afirka a matsayin nahiya mai cike da kyawawan damammaki, wadda ta cancanci cimma burin neman ci gaban tattalin arziki mai dorewa.
Sisi ya kuma kara da cewa, Afirka na da albarkar yawan jama'a da arziki, wanda kuma kalubale ne na samun zaman rayuwa mai kyau ga dukkanin jama'ar nahiyar.(Murtala Zhang)