in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin bude cibiyar bayar da bizar kasar Sin a kasar Masar
2018-12-18 10:20:56 cri
An yi bikin kaddamar da cibiyar bayar da takardar bizar kasar Sin jiya Litinin a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar, al'amarin da ya nuna cewa, tun daga ranar, dukkanin mutanen kasar Masar da suke dauke da fasfo na gama-gari, da fasfo na aiki, wadanda ke son ziyartar kasar Sin cikin wani kankanin lokaci, ko kuma halartar darussan horaswa, za su iya neman samun biza ta zuwa kasar Sin a wannan cibiya.

Da yake tsokaci yayin bikin bude cibiyar, jakadan kasar Sin dake Masar Song Aiguo, ya ce a 'yan shekarun nan, ana kara samun fahimtar juna tsakanin Sin da Masar a fannin siyasa, kuma mu'amalarsu ta fannonin tattalin arziki, da kasuwanci, da al'adu na dada ingantuwa. Ya ce kafa irin wannan cibiya ta bayar da takardar bizar zuwa kasar Sin, ya shaida babban ci gaban dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, kana wani muhimmin mataki ne da ofishin jakadancin Sin dake Masar ya dauka, na saukakawa mutanen Masar matakan ziyara kasar Sin.

Rahotanni daga ofishin jakadancin Sin dake Masar sun ce, adadin yawan mutanen Masar da suke neman samun takardar bizar zuwa kasar Sin na karuwa a kowace shekara, kuma a bana, adadin yawan mutanen Masar da suka samu bizar zuwa kasar Sin a ofishin jakadancin Sin ya zarce dubu 43.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China