A watan Yunin shekarar 2019 ne, za a gudanar da gasar cin kofin kwallon kafan Afirka, gasar da ake sa ran kasashe 24 na nahiyar za su halarta a wannan karo.
Kafin hakan, an soke iznin daukar bakuncin shirya gasar da a baya aka baiwa kasar Kamaru, saboda hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirka tana ganin cewa, kasar Kamaru ba za ta iya shirya gasar kamar yadda ake bukata ba, daga baya ne kasashen Masar da Afirka ta Kudu suka nuna aniyarsu ta karbar bakuncin gasar.
Kasar Masar ta taba zaman zakara sau 7 a tarihi a gasar cin kofin kwallon kafan Afirka. (Zainab)