Kwamandan hukumar na jihar, Buba Wakawa ne ya bayyanawa Kamfanin dillancin labaran Nijeriya a yayin da suke zantawa. Ya ce, sun kama ne a lokacin da suka fita wani zagaye na musamman wanda suka yiwa take da "Operation Narco X'' a jiya Laraba.
Wakawa, ya roki gwamnatin jihar Edo da ta rika tallafawa hukumar ta su ta hanyar ba su motocin hawa wanda zai taimaka musu wajen dakile masu irin wadannan miyagun ayyuka a jihar. Ya ce, musamman a irin wadannan lokuta na taruka da bukukuwa.
Kwamandan NDLEA din ya kara da cewa, daya daga cikin manyan masu safarar wadannan kayayyakin ya shiga hannunsu, kuma yana taimakawa hukumar jihar wajen binciken da suke gudanarwa. (Labarin da aka samu daga jaridar Leadership)