Joyce Ndalichako ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi, yayin bikin ban kwana da daliban da suka samu irin wannan dama, wanda ya gudana a birnin Dar es Salaam.
Ministan ya ce Sin ta nunawa duniya matsayinta na kasancewa abokiya ta gari, ta hanyar tallafawa Tanzania a fannoni da dama, ciki hadda hanyar bunkasa ilimi da horas da jami'an kasar. Ya ce yana farin cikin ganin kasarsa ta samu wannan dama, duba da cewa jami'an da za su samu horo a kasar Sin sun fito ne daga sassan da ake matukar bukatar hidimar su.
Jami'an lafiya da za su samu horo karkashin wannan dama da Sin ta tanadarwa Tanzania a wannan karo, sun hada da ma'aikatan lafiya masu aikin dashen bargo, da masu dashen koda, da kwararru a fannin kula da lafiyar jini, da masana fannin likitancin magunguna. (Saminu Hassan)