in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar da wasu kasashen Afirka sun shirya wani atisayen soja kan yaki da ta'addanci
2018-12-10 10:33:37 cri
A jiya ne rundunar sojan kasar Masar da wasu kasashen Afirka suka fara wani atisayen soja na hadin gwiwa game da yaki da ayyukan ta'addanci.

Da yake karin haske cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, mai magana da yawun rundunar sojan kasar Masar Tamer al-Refaie ya bayyana cewa, rukunin farko na kasashen nahiyar Afirka dake yankin Sahel (CEN-SAD) da za su gudanar da atisayen da kasar ta Masar, sun hada da kasashen Sudan da Najeriya da Burkina Faso.

Ya ce, wannan shi ne karo na farko da za a gudanar da irin wannan atisaye a kasar Masar. Manufar atisayen dai ita ce kara karfin alakar sojojin Masar da takwarorinta na kasashen Afirka da samar da hadin kai tsakanin dakarun musamman na Afirka dake yaki da barazanar ta'addanci.

Kakakin ya kara da cewa, atisayen zai kuma horas da dakarun dabarun tunkarar barazanar ta'addanci daban-daban kamar kungiyoyin 'yan tawaye, da yadda za su kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su, da ma yadda za su yi aiki tare da sauran dakarun kasashe kawaye.

Ya kuma lura da cewa, an kasa kasashen dake yankin Sahel (CEN-SAD) zuwa wasu kungiyoyi ta yadda za su gudanar da makamancin atisayen a ranaku daban-daban kamar yadda aka tsara cikin jadawali da zai kunshi dukkan kasashe.

Sanarwar ta kara a cewa, atisayen na fatan karfafa tsaro da zaman lafiya a Afika, wajen yakar duk wasu barazana da kalubale.

Arisayen wanda za a kammala a ranar 14 ga watan Disamba, za a gudanar da shi ne a sansanin sojan Masar na Mohamed Naguib, sansani mafi girma a yankin gabas ta tsakiya da Afirka, wanda ke lardin Matrouh na Bahar Rum din Masar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China